Ilimin Naura mai kwakwalwa(gabatarwa)

Assalamu alaikum ‘yan’uwa daliban ilimi barkammu da kasancewa a wannan gida namu mai tarin albarka, gidan ilmantar da al’umma gami da fadakarwa tare da nishadantarwa.
Muna farin cikin fara gabatar muku da shirin ILIMIN NA’URA MAI KWAKWALWA wato computer (ILIMIN COMPUTER).
Idan mun lura da kyau yanayin rayuwarmu a yau ta zama sai da wannan na’ura (computer)
Neman aiki ka ke yi ko makaranta (jami’a),
Tafiya za ka yi (kasar waje) ko bincike
Kusan duk wadannan abubuwa sai da computer, wasun suma basa yuwuwa sai da computer
Kusan dai ka iya cewa computer ta zama lalurar rayuwarmu a yau, ma’ana idan kana bukatar fadada tunaninka, da sabunta wayewarka da sanin inda wannan Duniya tasa gaba cikin lokaci, batare da anbaka a bayaba, toh lallai kana da bukatar sanin ILIMIN COMPUTER
Hakan tasa wannan gida (Hausa Prints) ya kirkiri wannan shiri na ILIMIN COMPUTER dan kokarin ganin al’ummarmu sun yi rayuwa cikin wayewa, kuma sun tafi kafada-da-kafada da zamani.
Wannan shiri (ilimin computer) zai koyar da mu ne, yadda zamu mu’amalanci yanar gizo (Internet), da ita kanta computer, da sauran duk abin da ke da alaka da ita (computer).
Ku kance da F dan ilmantarwa da wayar da kai akan bangarorin al’amuran rayuwa.



Ku kasance a wannan gida mai albarka dan samun shirye shiryan mu masu nishadantarwa.

Post a Comment

0 Comments