Abinda Yake Tsakanina Da Jamila Nagudu - Maifata


Mene ne tarihinka a takaice?

Haruna Maifata: Sunana Haruna Talle Maifata, amma ana kirana da Sardaunan Samarin Arewa, takena ne a masana’antar fina-finan Hausa. An haife ni a Jos, na yi makarantar firamare ta St. Paul Primary school a Jos, na yi sakandare a Usama Arabic Secondary School, sannan na yi difloma a kwas din koyon aikin jarida a Jami’ar Jos. A bangaren iyali ina da mata daya da ’ya’ya uku.





Me ya ja hankalinka ka shiga harkar fim?
Ka san fim abu ne na sha’awa, za ka samu yara da matasa musamman ma mata suna sha’awar fim, akwai yayana sunansa Baban Umma Talle Maifata, shi mai shirya fim ne, kuma ina ganin yadda ’yan fim suke da farin jini a wurin mutane. To a wannan lokacin sai ya yi mini alkawarin zai sanya ni a wani fim da yake so ya yi. Na sa raina sosai a kan fim din, amma kuma bai sanya ni a ciki ba. Hakan ya sa raina ya baci, sai na yi tunani ai harkar fim fa harka ce da idan kana da kudi a wannan lokaci za ka iya yin ta.
A wannan lokacin sai na samu jarumi kuma darakta Bello Muhammad Bello, na ce zan dauke shi aiki, na ce zai yi mini daraktin fim dina, bayan ya karanta labarin fim din sai ya zaba mini rol din da ya kamata in hau saboda ni sabon jarumi ne, sunan fim din ‘Zuciyata’, Muka yi fim din kuma ya karbu sosai.
Zuwa yanzu ka yi fina-finai nawa?
Ni jarumi ne, kuma mai shiryawa ne, akwai fina-finan da na shirya a kamfanina da kuma wadanda na fito na wasu kamfanoni. A kamfanina na yi fina-finai 42, kama daga fim dina na farko ‘Zuciyata’ zuwa na karshe da na yi mai suna ‘Farida Nabeel.’ Amma dangane da fina-finan sauran kamfanonin da na fito a ciki, a gaskiya ban san adadinsu ba.
Ko za ka kawo kadan cikin fina-finan kamfaninka?
Ka ga akwai ‘Zuciyata’ da ‘Hafsat ko Safiya’ da ‘Kundin Tsari’ da ‘Farin Sani’ da ‘Tawakkaltu’ da ‘Ran Gini Ran Zane’ da ‘Kura Ta ci Kura’ da ‘Sababi’ da ‘Ta Cuce Ni’ da sauransu.
A cikin fina-finan kamfaninka 42 wanne ne ya fi shiga ranka?
Ina son dukan fina-finaina saboda idan aka kawo mini labarin fim sai na duba shi, idan na ji ya shiga zuciyata sai in karbe shi. Ba zan manta ba, akwai wani fim dina mai suna ‘Ran Gini Ran Zane’, a lokacin mun samu sabani da daraktana saboda wasu dalilai sai daraktan da yake ba da umarni a fim din, ya ki zuwa wurin daukar fim din, bai zo ba tun safe muna jiransa har karfe 4 na yamma. Hakan ya sa ban ji dadi ba, karshe na nemi wani darakta.
Daga nan sai na fara ba da umarni a kan wani fim dina mai suna ‘Tawakkaltu,’ bayan na yi fim din sai ya karbu fiye da kowane fim dina a wannan lokacin, bayan na gama shi, sai na ga cewa zan iya in rika fitowa a fim kuma in rika ba da umarni, duk da cewa kowane bangare rike shi da wahala, musamman ma darakta. Hakan ya sa na zama kamar dan wasan kwallon kafa da ake kira koci-kuma-dan-wasa.
Fim din da ya shiga mini rai kuwa shi ne, fim din da idan na fada maka kudin da aka kashe sai ka yi mamaki, domin bai kai kudin da ake biyan wani jarumi daya ba. A layinmu aka yi fim din, fim ne a kan talakawa, sunan fim din ‘Farmaki,’ fim ne a kan sara-suka, kodayake fim din ya zo da batun fashi da makami, inda aka kashe iyayen jarumin fim din. Da ya dawo cikin unguwarsu sai aka tsane shi, sai hakan ya sa ya rika boye fuskarsa yana kashe mutane.
Bayan fim din ya fito kasuwa akwai wani abokina a Kano, sunansa Auwalu Gadon kaya, abokin kasuwancina ne, sai ya ce mini ya kamata in shiga gasa da fim din, sai na ki, daga karshe dai ya tilasta mini na amince, shi ne ma ya cika mini fom na shiga gasar. Shi ya yi komai na gasar, sai aka sanya ni a cikin rukunin rol din mugunta.
Ko ranar da za a yi bikin gasar karfe goma na daren ranar, amma karfe biyun rana ma ina Jos, kuma za a yi bikin a Abuja, na dawo ina kwance abina, saboda ban sa rai ba, amma haka abokaina suka tilasta mini sai na je. Haka dai muka tafi Abuja, ni dai ban sa rai ba, saboda a lokacin abokan karawata su ne, jarumi Adam A. Zango da kuma Tanimu Akawu, na san fim din da Zango ya shiga gasar da shi, kudin da aka kashe a fim din ya fi nawa, haka ma na bangaren fim din da Tanimu Akawu ya shiga gasar da shi.
Ko lokacin da muka shiga dakin taron ma sai ni da Sadik Ahmad muka koma can baya, mun ki zama a wurin da aka tanada don jarumai da sauran masu fada-a-ji a masana’antarmu, ba mu ankara ba ashe Ali Nuhu ya ganmu, sai ya zo wurinmu sannan ya fara mana fada a kan muna ware kanmu, haka ya sa muka koma wurin da aka tanada mana, ni dai ina ta dari-dari. A takaice dai na yi farin ciki mara misaltuwa a lokacin da aka ambaci ni ne na lashe gasar, na kasa tsayawa tsabar murna, hakan ya sa ba zan manta da fim din ba, ya shiga raina sosai.
Wadanne abokan sana’arka ka fi jin dadin aiki da su?
A maza ina jin dadin aiki da Ali Nuhu saboda idan aka ce za a fito karfe 7 na safe, to yana rike wannan alkawarin, sannan akwai Sadik Ahmad shi ma yana ba ni shawara sosai.
A mata kuma akwai Fati Zinariya, ita kuma ta fi so ta yi amfani da kayanta, sannan idan za ta yi kwalliya komai launi iri daya take sawa, wato tun daga agogo har takalmi iri daya ne.
Ana yawan ganin jaruma Jamila Nagudu a fina-finan kamfaninka, har wadansu sun fara zargin kuna soyayya, ko me za ka ce a kan haka?
Ita Jamila mutum ce mai saukin kai, kuma ta iya aktin, tana kokari, idan aka ce mata za mu fito a fim tare to tana dagewa, saboda idan ina yi fim kamar dan wasa Cristiano Ronaldo nake yi, kafar hagu tana ba da wuta, ta dama ma tana ba da wuta. Ta iya aktin, tana ba da abin da darakta yake so, sannan tana da saukin kai, shi ya sa nake sanya ta sosai a fina-finan kamfanina, amma babu soyayya tsakanina da Jamila Nagudu.
Yanzu wadanne matsaloli kake fuskanta?
Duk wani abu da dan Adam ya yi nasara to sai ya fuskanci matsaloli, amma abin da na sani shi ne ba na yarda matsalolin su tayar mini da hankali. Don haka ban cika ambaton kalubale ba, domin yawanci duk abin da mutum zai yi a rayuwa ba wai fim ba sai ya fuskanci kalubale. Duk hanyar nasara akwai kalubale.
Yawancin ’yan fim masu aure musamman maza sukan fuskanci matsala da matansu, saboda yadda dimbin masoyansu mata suke ziyartarsu ko kiransu a waya, ko ka fuskanci matsala makamanciyar haka?
Ina da masoya mata fiye da yadda ake tunani, kuma na auri matata ina fim, ta san sana’ata a lokacin da na aure ta. Tunda nake da ita ban taba samun rana daya da ta yi yaji ba, saboda ban boye mata komai ba, kuma ta yarda da ni. Akwai lokacin da na yi wata daya ba na Jos, ta san fim nake yi kuma akwai mata da yawa a wurin daukar fim din, amma ba ta zarge ni ba.
A lokuta da dama nakan bar wayata a gida, kuma ta san lambobin sirrin wayar, tana duba wayar, akwai yarda tsakanina da ita.
Bari ma in fada maka wani abu, a gidana akwai dakuna da yawa, akwai gefena da kuma dakin ’ya’yana da na matata, sannan akwai sauran dakuna, wani lokaci idan zan yi fim in har na kira wadansu jarumai musamman ma mata da zan kashe kudi sosai wajen kama otal, sai in roke su zo gidana tunda akwai dakunan da za su kwana. Jarumai mata da yawa da muka yi aiki da su sun kwana a gidana, idan har da rashin yarda ko zargi matata ba za ta amince su kwana ba. Akwai lokacin da na ba matata kudi ta yi fim dinta na kanta, ta zabi jarumai mata da take so su fito a fim din, inda kuma suka kwana a gidanmu, har ta kai an dauki wani bangare na fim din a gidana.

Daga : Aminiya







Post a Comment

0 Comments