Yan mintuna ne kadan suka wuce sha biyun dare, mata da ‘ya ‘ya sun dade da yin barci. Amma yin barci ba nawa bane, domin dole ne in gano abin da ya sa code da na rubuta a Kwamfuta don kirkiran wani shafi a yanar gizo da zai dinga nuna wa duk wanda ya leka shafin bayyanai akan hasashen yanayi bai yi aiki ba.
Na sake duba code din, na yi gyare-gyaren da na ga yakamata, na sa ke gwadawa ko wannan karon zai yi aiki.
Idan na danna nan, ya kamata ya nuna min wani akwatin da zan sanya garin da nake son in sami hasashen shi. Na sanya, na danna amma kash.. sai dai na kara duba code din……..
YANDA PROGRAMMING YA ZAMA ABUN SHA’AWA A WURI NA.
Na fara koyon computer programming ne shekaru takwas da suka wuce, daga wani abokin aiki na da shima ya dade yana yi.
Yana yawan bani mamaki yarda na gan ya na kirkiran shafin yanan gizo da harshen programming da aka fi sani da HTML da CSS. A tun wanan lokaci ne ni ma na sami sha’awar.
A bangaren kimiya da fasaha, mutanen sun kasu kashi biyu, wa’inda suke kirkira, da kuma masu amfani da abin da aka kirkira. Tun ina karami ne na ginu da sha’awar kirkirar abinda mutane za su yi amfani da shi.So dayawa ina yawa amfani da shafufuka irin su facebook, twitter, mujallalu, Kwamfuta program da sauransu, kuma ina yawan mamaki sanin cewa, wani ne a wani bangaren duniyar nan da muke ciki, ya zauna ya kirkire su.hi yasa na dauki matakin ni ma in bi duk matakin da ya kamata wajen samun ilmin da zan fara kirkirar programs ko applications da mutanen zasu amfani da shi.
Kash… sai dai da na fara, nan na fahimci ai koyar programming na da wuya, domin yana bukatar lokaci da maida hankali sosai, domin mai koyo zai dinga karo da kalmomi da ya saba amfani da su da wa’inda ma bai saba ba.
Kuma kowani harshen programming cikin daruruwa da ake da su kamar su JavaScript, Python, PHP, C, C++, C##, na da yarde kowane ya saru akai.
AMMA WUYAR ABU BATA HANA AYI
A kalmar maragayi sohon shugabar Amurka John F. Kennedy, yace
“Mun zabi muje mu gan yarda Watã take ne, ba domin yana da sauki ba, amma domin yana da wuya, domin wanan burin za su sa mu gwada abin da manyan injiniyoyin mu za su iya yi, domin mu nuna za mo iya kuma mu san zamu iya, kuma ba abin da zamu jinkirta bane”.
Ana yawan amfani da kalmar wuya wurin nuna wahalar abu ko abin da ba’a so, ta bagaren rashin lafiya, ko tattalin arziki. Amma koyar abin da ke da wuya yana da amfani sosai.
Ilimin Likitanci na da wuyar koyo amma da amfani, haka ma ilimin kimiya da fasaha, ilimin shariya da sauransu. Haka ma ya ke da koyar Computer programming.
Duk da Computer programming ya na da bagare dayawa, mai ilimin sa yana da ikon kirkira programs da applications da mutane za su amfana da shi irin su facebook, twitter, micorsoft word da sauransu.
Idan Allah ya taimaka ka/ki kirkiri abin da jama’a za su amshe shi hanu biyu suyi amfani da shi, alheri ne a gare ka/ki kuma zai sa kaza ma ficcecen mai kirkira irin su Mark Zuckerberg (facebook), Bill Gates (Microsoft), Aminu Bakori (Payant) da sauransu.
Wuyar yin shi kada ta hanaka, ka fara kawai, kuma ka maida hankali, idan ka fuskanci wuya a cikin shi, kada ka daina, yana nufin kana kan hanya.
0 Comments